Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, ana gabatar da wannan jerin bahasin Mahdawiyya mai taken “Zuwa Ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yada koyarwa da ma’arifofi da suka shafi Imamuz Zaman (A.F) ga ku masu ilimi da daraja.
Nazari da bin diddigin addu’o’in Mahdawiyya na bayyana mana wani hoto na matsayi da darajojin wannan Mai girma (A.F), kuma yana buɗe ƙofar sani (ma’arifa) ga masu imani da shi. Ga wasu daga cikin waɗannan matsayai:
Khalifatullah (Kalifan Allah), Hujjatullah (Hujjar Allah)
A cikin Ziyarar Aali Yasin an kawo cewa:
«السَّلَامُ عَلَیکَ یا خَلِیفَةَ اللَّهِ وَ نَاصِرَ حَقِّهِ، السَّلَامُ عَلَیکَ یا حُجَّةَ اللَّهِ وَ دَلِیلَ إِرَادَتِه.»
"Aminci a gare ka, ya khalifan Allah kuma mai taimakon haƙƙinsa, aminci a gare ka, ya hujjar Allah kuma jagoran nufinsa."
A bayyane yake cewa matsayin khalifatullah da kasancewa hujjar Allah, yana daga cikin mafi girman matakai da Allah Ya tanadar wa Imam Mahdi (A.F). A wannan matsayin, a zamaninsa babu wanda ya yi kamarsa; shi ne na musamman.
Babullah (Ƙofar Allah), Sabilullah (Hanyar Allah)
A cikin Ziyarar Ali Yasin muna karantawa:
«السَّلَامُ عَلَیکَ یا باب الله.»
"Aminci a gare ka, ya ƙofar Allah."
Haka kuma a cikin Ziyarar Sahibul Amr (A.F) muna karantawa:
«السَّلَامُ عَلَیکَ یا سَبِیلَ اللَّهِ الَّذِی مَنْ سَلَکَ غَیرَهُ هَلَک.»
"Aminci a gare ka, ya hanyar Allah, wadda duk wanda ya bi wata hanya ba ita ba, ya halaka."
Fassarar “Babullah” na nuna wannan hakika cewa duk wanda yake son ya kai ga Allah, ya bi umarninsa, kuma ya samu yardarsa, dole ne ya bi hanyar imani da Imam Mahdi (A.F), imani da imamancinsa, da cikakkiyar biyayya gare shi. Haka ma kalmar “Sabilullah” tana nuna cewa hanya ɗaya tilo ta kaiwa ga Allah da kusancinsa ita ce imani, i'itiƙadi, da biyayya ga Waliyin Allah; wato Imamuz Zaman (A.F).
Mithaƙullah, Wa‘adullah
A cikin Ziyarar Ali Yasin ana cewa:
«السَّلَامُ عَلَیکَ یا مِیثَاقَ اللَّهِ الَّذِی أَخَذَهُ وَ وَکَّدَهُ، السَّلَامُ عَلَیکَ یا وَعْدَ اللَّهِ الَّذِی ضَمِنَه.»
"Aminci a gare ka, ya alƙawarin (mithaƙ) Allah da Ya karɓa kuma Ya ƙarfafa, aminci a gare ka, ya alƙawarin (wa‘ad) Allah da Allah Ya tabbatar da shi."
“Mithaƙullah” na nufin Imam Mahdi (A.F) shi ne cikakken bayyanannen ma’anar alƙawari da Allah Ya ɗauka daga bayinsa, kuma alƙawarin mutane da Imam Mahdi (A.F) yana daidai da tsayuwar su a kan dukkan addini da shari’ar Allah. Kamar yadda barinsa da rabuwa da shi yake kamar take dukkan alƙawurran Allah.
“Wa‘adullah” kuma na nufin Imam Mahdi (A.F) shi ne bayyanannen misalin alƙawarin Allah a Alƙur’ani game da mulkin salihai da yaɗuwar ƙima da alheri a doron ƙasa. Shi ne babban mabuwayi na Allah da aka yi wa alkawari; bayyanarsa ita ce cikar burin dukkan Annabawa da Waliyyai, kuma mai farfaɗo da shari’a da littattafan sama. Hakika shi ne alƙawarin Allah da aka tabbatar, kuma mabuwayi tabbatacce da aka ambata a littattafan sama; babu abin da zai hana bayyanarsa.
Aynullah an‑Nazirah
A cikin wata addu’a da aka ruwaito daga Imam Ridha (A.S) an ce:
«وَ عَینِکَ النَّاظِرَةِ عَلَی بَرِیتِکَ وَ شَاهِدِکَ عَلَی عِبَادِک.»
"Shi ne idonka mai gani a kan halittunka, kuma shi ne shaidarka a kan bayinka."
Waɗannan kalmomi na nuna cewa Imam Mahdi (A.F), a matsayin hujja kuma wakilin Allah, shi ma mai sa‑ido (mai lura) ne na Allah; ayyukan mutane a bayyane da a ɓoye ba sa buya a gare shi, a’a, shi mai shaida ne mai kallo a kan dukkan ayyuka. Yin imani da wannan gaskiya yana taimakawa ƙwarai wajen tarbiyyar kai, tsarkakewa, da gyaran ɗabi’a.
A cikin wata riwaya daga Imam Mahdi (A.F) an ruwaito cewa ya ce:
«فَإِنَّا نُحِیطُ عِلْماً بِأَنْبَائِکُمْ وَ لَا یعْزُبُ عَنَّا شَیءٌ مِنْ أَخْبَارِکُم.» (الإحتجاج، ج ۲، ص ۴۹۵)
"Lallai Ilminmu ya kewaye labaranku da halayenku, kuma babu wani abu daga labaranku da yake ɓoyuwa a gare mu." (Al-Ihtijaj, juzu'i na biyu, shafi na 495)
Da sauransu…
Wannan tattaunawa zata ci gaba…
An ciro daga littafin Negine Afarinesh, tare da ɗan gyara
Ra'ayinka